Kakakin yan Sandan birnin Bashir Mujahid ya bayyana cewar an ji karar makamin roka da kuma bindigogi a cikin Cibiyar da ake kira Marshal Fahim Military Academy.
Bayanai sun ce an hallaka mutane da dama a harin dake zuwa kwana guda bayan wani kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 100 a birnin.
Kungiyar Isil ta sanar da daukar alhakin kazamin harin Cibiyar horar da soji na Kabul a Afghanistan